Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorizedWani dan Majalisar wakilan Nijeriya daga PDP ya sauya sheka zuwa jam'iyyar...

Wani dan Majalisar wakilan Nijeriya daga PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

 

Majalisar wakilan Nijeriya

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Jaba/Zango Kataf a jihar Kaduna, Amos Magaji, ya shirya sauya sheka ne bisa rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya.

Kakakin majalisar Tajudeen Abbas wanda ya jagoranci zaman majalisar a ranar Talata ya karanta wasikar sauya shekar Magaji a zauren majalisar.

Magaji ya ce rikicin da haryanzu ba a warware a PDP ba tun daga matakin kasa har zuwa jiha ya sa ba zai iya zama a cikin jam’iyyar ba.

Magaji dai shi ne dan jam’iyyar PDP na uku da ya koma APC tun bayan kaddamar da majalisar ta 10 bayan Chris Nkwonta da Eriatheke Ibori-Suenu, daga jihohin Abia da Delta.

Da yake nuna adawa da sauya shekar, shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, ya bukaci kakakin majalisar da ya ayyana kujerar dan majalisar na Kaduna a matsayin wadda babu kowa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata