DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sanda sun kama mutane uku da ake zargin da lalata wayoyin lantarki a Adamawa

-

 

Police

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutane uku da ake zargi da lalatawa da kuma satar wayoyin na’urar raba lantarki a Wuro Dole da ke karamar hukumar Girei a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Yola, babban birnin jihar.

Ya ce kamen ya biyo bayan sahihan bayanai da suka samu daga wata majiya mai tushe, wanda ya kai ga cafke wasu mutane uku da ake zargi da satar wayoyin wutar lantarki da ke samar da wuta a sassan Girei.

Wadanda ake zargin, Rabiu Ali mai shekaru 28, sai Muhammad Musa mai shekaru 42, da Abubakar Usman mai shekaru 18, sun hada baki da wasu mutum uku waɗanda har yanzu ana nemansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara