Wednesday, April 8, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin ka an yi rashawa da cin hanci da fama da matsalolin...

Gwamnatin ka an yi rashawa da cin hanci da fama da matsalolin tsaro -jigo a APC ya mayarwa Buhari martani

 

Muhammadu Buhari

Wani jigo a jam’iyyar APC Josef Onoh, ya ce shekaru takwas da tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya yi a kan karagar mulki na tattare da cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro.

Onoh ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani ga Buhari na cewa Nijeriya ta samu ci gaba sosai a harkokin tsaro da tattalin arziki a lokacin mulkinsa.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa lokacin da ya  karbi mulki tattalin arzikin Nijeriya ya rushe tare da matsalar tsaro a hannun jam’iyyar PDP da ta shafe shekaru 16 tana mulki.

Buhari, ya tabbatar da cewa a dabarun gwamnatinsa sun yi nasarar magance wadannan matsaloli, tare da dakile ayyukan ta’addanci da matsalolin tattalin arziki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata