Taron kaddamar da jam’iyyar ADC da hadakar ‘yan adawa suka shirya ya gamu da cikas bayan da wani Otal ya dakatar da shi bisa wasu dalilan sa na cikin gida, kamar jaridar Punch ta ruwaito.
Taron da aka shirya kammadar da jam’iyyar ta ADC mai kudurin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben shekarar 2027, ya fuskanci tsaiko ne bayan da hukumar gudanarwar Otal din ta sanar da masu shirya taron batun dakatarwar tare da basu hakuri.
Wannan mataki dai ya jawo suka daga tsagin ‘yan adawa tare da zarge zargen kutse na siyasa daga gwamnatin APC, bayan sanannen dan jarida, Dole Momodu dake goyon bayan hadakar kawancen jam’iyyun ya wallafa hoton takardar soke taron.
Sai dai ya ce hakan ba zai sa su yi kasa a gwiwa ba a yunkurin su na kalubalantar jam’iyya mai mulki.
