DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Tarayya ta ce nan da wasu ‘yan watanni za a kara kudin wutar lantarki a Nijeriya

-

 

Shugaba Tinubu

Mai baiwa shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ta bayyana haka a taron shugabannin kasashen Afirka kan makamashi da aka yi a Dar es Salaam na kasar Tanzania, inda Nijeriya ta gabatar da wani shiri na dala biliyan 32 da nufin bunkasa wutar lantarki nan da shekarar 2030.

A cewarta Nijeriya na kokarin warware yin wasu sauye sauye masu inganci don jawo hankalin masu zuba jari zuwa kasar musamman ta fuskar makamashi.

Ta ce daya daga cikin manyan kalubalen da ake neman warwarewa a cikin ‘yan watanni masu zuwa shine canza farashin wutar lantarki don ci gaba da samun kudaden shiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara