DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar kula da ‘yan sandan Nijeriya ta umurci duk wani jami’i da ya haura shekaru 60 da yayi ritaya

-

 

Kayode Egbetokun

Google search engine

Umurnin na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da jaridar Daily Trust ta yi rahoto kan wani sabon cece kuce da ya kunno kai a cikin rundunar ‘yan sandan kan karin wa’adin aikin da aka yi wa Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun bayan ya cika shekaru 60. 

A cikin wani sabon rahoto da jaridar ta buga a ranar Juma’a, hedikwatar rundunar tare da babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, sun tabbatar da cewa ci gaba da zaman Egbetokun a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sandan yana kan doka.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, kakakin hukumar ta hukumar kula da ‘yan sandan Nijeriya PSC, Ikechukwu Ani, ya bayyana cewa wannan matakin ya zama tilas saboda hukumar ba ta son ya zama ana saba wa doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalilin da ya sa muka maye gurbin rundunar Operation Safe Haven da Enduring Peace – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Enduring Peace domin magance matsalar tsaro da ta...

Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya, Solomon Arase, ya mutu

Solomon Arase mai shekara 69 ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin Cedar Crest da ke Abuja, babban birnin tarayya.Wani ɗan uwansa ya tabbatar...

Mafi Shahara