Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuWasu ‘yan jam’iyyar hadaka ta ADC sun maka sabbin shugabannin rikon kwarya...

Wasu ‘yan jam’iyyar hadaka ta ADC sun maka sabbin shugabannin rikon kwarya a Kotu

Wasu mambobin jam’iyyar ADC guda uku sun shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, suna ƙalubalantar sahihancin nadin sabbin shugabannin rikon kwarya da tsohon shugaban majalisar fattawa, David Mark ke jagoranta.

A cikin ƙarar da suka shigar ranar 4 ga Yuli, masu ƙara shigar da karar Adeyemi Emmanuel, Ayodeji Tolu, da Haruna Ismaila, sun nemi kotu ta tantance halascin nadin sabbin shugabannin jam’iyyar da suka ce an yi ba bisa ka’ida ba.

Sun bayyana cewa tsohon shugaban jam’iyyar, Nwosu, bai da hurumin kiran taron NWC ko NEC ko wani taron jam’iyyar kasancewar wa’adinsa ya ƙare, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Sun kara da cewa nadin David Mark, Rauf Aregbesola, da Bolaji Abdullahi a matsayin shugabanni na rikon kwarya bai da madogara a doka, don haka suna neman kotu ta ayyana nadin a matsayin maras inganci, sun roki kotu ta hana INEC amincewa da su a matsayin shugabannin jam’iyyar na rikon kwarya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata