Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuAkwai Gwamnonin APC da wasu jiga-jiganta da ke goyon bayan hadakar ADC...

Akwai Gwamnonin APC da wasu jiga-jiganta da ke goyon bayan hadakar ADC – Babachir Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa wasu gwamnoni da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na goyon bayan hadakar jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar ADC, a boye don zaben 2027 da ke tafe.

Babachir, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na TVC a ranar Talata.

Ya ce akwai ‘yan APC da dama da ke goyon bayan wannan hadaka amma suna boye wa saboda rashin jarumtar fitowa fili su fadi gaskiya kamar yadda shi ya yi.

A cewarsa, cikin masu goyon bayan hadakar ADCn har da gwamnoni wadanda ke aiki tare da wannan sabuwar tafiyar adawar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata