Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa babu wani yunkuri daga gareta na karya dimokuraɗiyya, tana mai jaddada cewa burinta kawai shi ne ceto Najeriya daga rashin iya tafiyar da mulki na gwamnatin APC ƙarƙashin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sakataren Yaɗa Labarai na riko na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana mamakinsa kan yadda jam’iyyar APC ke fargabar tasirinsu, yana mai cewa hakan na nuna kamar ta mance da ainihin dalilan kafuwar hadakar ADC.
A ranar Talata, ne mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin labarai da dabarun siyasa, Bayo Onanuga, ya yi zargin cewa wasu manyan ’yan siyasa na ƙulla makircin kifar da gwamnatin Tinubu kafin zaɓen 2027.
Sai dai a martaninta, jam’iyyar ADC ta ce wannan wallafa rashin kishin kasa ce kuma ƙarya ce, tana mai gargadi cewa irin waɗannan kalamai na iya zama ƙwarin gwiwar murɗe dimokuraɗiyya da far wa ’yan adawa kamar yadda jaridar Punch ta ambato.
