Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ’yan majalisa ba su zo majalisa don tara kudi ba, sai dai don bayar da gudunmawa da sadaukarwa ga ci gaban al’umma da kuma makomar ’yan Najeriya masu zuwa.
Akpabio ya fadi haka ne a zauren majalisa yayin zaman majalisar na ranar Laraba, yayin da yake tofa albarkacin baki a muhawarar kudirin gyaran dokar wutar lantarki ta 2023, wanda Sanata Enyinnaya Abaribe (APGA, Abia South), shugaban kwamitin lantarki na majalisar dattawa ya dauko.
Akpabio cikin rahoton Daily Trust ya kara da cewa babu ci gaban masana’antu ko tattalin arziki da zai samu a kasar nan ba tare da ingantacciyar wutar lantarki ba, don haka ana bukatar gyare-gyare da sauyi mai zurfi a fannin.
Kudirin, idan aka amince da gyaransa, zai fayyace batun sauya ikon kula da harkokin wutar lantarki daga Hukumar kula da wutar Lantarki ta kasa (NERC) zuwa gwamnatocin jihohi.

Allah yasa ayi Hakan Ameen