Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuKusan gwamnonin Nijeriya 10 ke shirin tsayawa takarar Sanata a 2027 -...

Kusan gwamnonin Nijeriya 10 ke shirin tsayawa takarar Sanata a 2027 – Daily Trust

Yayin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, rahotanni na nuni da cewa wasu daga cikin gwamnoni masu ci na shirin tsayawa takarar kujerun Sanata a mazabunsu.

Binciken da Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa akalla gwamnoni takwas na da niyyar tsayawa takarar Sanata daga jihohin da suke jagoranta, musamman wadanda ke kammala wa’adinsu na biyu kuma ba za su iya sake tsayawa takarar gwamna ba a 2027.

Gwamnonin da ke kan wa’adinsu na biyu sun hada da Abdullahi Sule na Nasarawa, Babagana Zulum na Borno, Bala Mohammed na Bauchi, Douye Diri na Bayelsa, Seyi Makinde na Oyo, Babajide Sanwo-Olu na Lagos, Dapo Abiodun na Ogun, Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, Mai Mala Buni na Yobe da Inuwa Yahaya na Gombe.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata