Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuDalilin da ya sa Sarki Sanusi bai halarci jana’izar marigayi Buhari ba

Dalilin da ya sa Sarki Sanusi bai halarci jana’izar marigayi Buhari ba

Majenin sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Muhammadu Dallatu, ya bayyana dalilin rashin ganin fuskar sarkin a jana’izar Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka yi a Daura sakamakon yana London kan wani aiki da ya tafi.

A cewar Dallatu, Sarkin zai dawo Najeriya ranar Laraba. Binciken da aka yi ya nuna Sanusi ya halarci gasar Access Bank Polo a Surrey, da ke Ingila, inda aka gan shi tare da fitattun mutane, ciki har da kocin kasar Ingila, Thomas Tuchel.

A daya bangaren, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya halarci jana’izar a Daura tare da wasu sarakuna daga jihar Jigawa, kamar yadda mai magana da yawunsa Abubakar Na’isa ya tabbatar.

A halin Yanzu dai rikicin shugabancin masarautar Kano yana ci gaba da tasowa, inda Sanusi da Aminu ke ci gaba da takaddama kan mallakar fada da kujerar sarautar birnin na Kano kamar yadda rahoton jaridar Punch ya Ambato.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata