Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuFicewar Atiku daga PDP ba zai girgiza mu ba - Gwamna Seyi...

Ficewar Atiku daga PDP ba zai girgiza mu ba – Gwamna Seyi Makinde

Gwamnan Jihar Oyo kuma mamba a Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP, Injiniya Seyi Makinde, ya bayyana cewa fitar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, daga jam’iyyar ba zai haifar da wata tangarda ba ga ci gaban jam’iyyar PDP.

Makinde ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin wata tattaunawa da manema labarai a birnin Akure, bayan da ya gabatar da jawabin musamman a wajen taron tunawa da cika shekaru 10 da naɗin sarauta na Mai Martaba Oba Aladetoyinbo Aladelusi, Deji na Akure.

Ya ce: “Ba na ganin hakan zai kawo koma baya ga PDP a matsayin jam’iyya. PDP cibiya ce, kowa na da ‘yancin shiga da fita yadda ya ga dama.”

A gefe guda kuma, Cif Bode George, ɗan kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya danganta fitar Atiku daga jam’iyyar da burinsa na zama shugaban ƙasa a 2027, wanda ya bayyana da cewa burin ya wuce kima.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata