Wasu tsofaffin jami’an ‘yan sandan Nijeriya suna gudanar da zanga-zanga a Abuja da Jalingo, babban birnin jihar Taraba, domin nuna damuwa kan rashin kulawa da walwalar su da ta sauran masu ritaya daga rundunar.
Zanga-zangar da aka yi a Abuja ta samu jagorancin shugaban fafutukar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, wanda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan halin da ‘yan sandan suka shiga, musamman game da biyan fansho da kula da rayuwar wadanda suka yi ritaya.
A wani bangare, Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya umurci kwamishinonin ‘yan sanda a jihohi da Abuja da su bayar da cikakken tsaro yayin zanga-zangar domin kare hakkin masu ritayar cikin lumana kamar yadda rahoton gidan talabijin na Channels ya ambato.
