Wednesday, April 8, 2026
HomeBabban LabarinmuKwankwaso ya yi ganawar sirri da Tinubu kan harkokin siyasa da shugabanci...

Kwankwaso ya yi ganawar sirri da Tinubu kan harkokin siyasa da shugabanci – Jaridar Punch

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban Nijeriya a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wata ganawar sirri da aka gudanar a gidan shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin. Jaridar Punch wadda ta ruwaito wannan labarin ta ce ganawar ta biyo bayan halartar Kwankwaso a taron Nigeria Forest Economy Summit 2025 da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa. Wannan shi ne karo na biyu da jaridu suka wallafa ganawarsu a fili cikin fiye da shekaru biyu.

Ganawar da suka yi a baya  ta faru ne a ranar 9 ga Yuni, 2023, kwana kadan bayan rantsar da Shugaba Tinubu, inda Kwankwaso ya ziyarce shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na farko daga ’yan adawa da ya kai wa Shugaba Tinubu ziyara. A wancan lokacin, ya bayyana wa ’yan jarida cewa sun tattauna batutuwan siyasa da mulki tare da shugaban kasa, kuma ya nuna yiwuwar yin aiki tare da shi, sai dai bai bayyana dalla-dalla ba. Ganawar da suka yi a wannan karo kuwa an gudanar da ita a boye, kuma fadar shugaban kasa ba ta fitar da bayani kan abin da suka tattauna ba kawo yanzu.

Lokacin da ganawar ta faru na da matukar muhimmanci, kasancewar tana zuwa ne makonni bayan jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) ta sanar da kafa wani hadin gwiwa mai fadi da nufin kalubalantar jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) a zaben 2027. Ko da yake jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP ba ta cikin hadakar da ADC ke jagoranta, rahotanni na nuna cewa shugabannin adawa na kokarin jawo Kwankwaso cikin tafiyar, suna ganinsa a matsayin fitaccen dan siyasa daga Arewa wanda zai iya taka rawa mai muhimmanci a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Kwankwaso, wanda ke da shekaru 67, ya dade yana taka rawa a siyasar Najeriya, kuma shi ne shugaban siyasar “Kwankwasiyya” mai mulki a jihar Kano, jiha mai matukar muhimmanci wajen lashe zaben shugaban kasa a Nijeriya. Kwankwaso, ya shugabanci jihar Kano sau biyu (1999-2003 da 2011-2015), ya taba rike mukamin Ministan Tsaro a lokacin shugabancin Olusegun Obasanjo, kuma ya tsaya takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP a 2023, inda ya zo na hudu amma ya lashe zaben Kano da gagarumin rinjaye. Jam’iyyarsa ta kuma lashe kujerar gwamna da mafi yawan kujerun majalisar dokokin jihar, lamarin da ya tabbatar da karfinsa a siyasance a jihar da ke da yawan al’umma mafi yawa a Arewacin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata