Jam’iyyar hadaka ta ADC mai adawa a Nijeriya, ta bayyana cewa gwamnoni na yi wa Shugaba Bola Tinubu karya game da matsalar tsaro da ke addabar kasar, tana mai ba da shawarar cewa lokaci ya yi da shugaban zai fita ya duba halin da ‘yan ƙasa ke ciki a tituna da ƙauyuka.
Jam’iyyar ta ce, akasin ikirarin da wasu jami’an gwamnatin Tinubu ke yi, musamman mai magana da yawun shugaban ƙasa Daniel Bwala, matsalar rashin tsaro har yanzu na cigaba da ci gaba a sassan ƙasar, musamman yankunan da ke fama da hare-hare, garkuwa da mutane da fashi da makami.
Mai magana da yawun ADC Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa idan ana son mafita ta gaskiya kan rikicin tsaro, shugabanci dole ya kasance cikin jama’a ba kawai cikin rahotannin gwamnoni ba.
