DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun yi ajalin ‘yan kasuwa tare da raunata mutum 11 a Fika a jihar Yobe

-

 

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni
Yan bindigar ana  zargin sun kai farmaki kasuwar da ke ci duk sati a Ngalda karamar hukumar Fika da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin da suka yi  harbe harbe tare da  fasa shaguna a kasuwar.
Wani dan karamar hukumar Fika Dauda Yakubu Damazai, ya shaida wa Daily Trust cewa wasu ‘yan kasuwa guda bakwai a babbar kasuwar shanun sun rasa rayukansu a wannan mummunan hari.
Ya ce da yammacin ranar wasu da ba a san ko su waye ba sun kai hari a kasuwar shanu da babbar kasuwar inda suka  kashe mutane bakwai tare da jikkata mutane 11, kuma tuni aka  garzaya da su babban asibitin Fika domin duba lafiyar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan majalisar wakilai 8 na LP da PDP sun sauya sheka a jihohin Delta da Enugu

A ranar Talata ‘yan majalisar wakilai takwas suka bayyana ficewa daga jam’iyyunsu zuwa wasu jam'iyyu daban-daban. ‘Yan majalisar wakilai 6 daga jihar Delta sun fice daga...

Gwamnatin tarayya ta fito da tsarin da zai kawo karshen wahalar da ake sha wajen tantance lambar NIN 

Gwamnatin tarayya ta amince da wani sabon tsari da hukumar dake bayar da katin dan kasa za ta rika amfani da shi don saukaka tantance...

Mafi Shahara