DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeUncategorizedRikakkun ‘yan bindiga biyu sun mika wuya tare da makamansu a jihar...

Rikakkun ‘yan bindiga biyu sun mika wuya tare da makamansu a jihar Katsina

 

Malam Dikko Umaru Radda

Wasu rikakkun ‘yan bindiga guda biyu a jihar Katsina sun mika wuya tare da makamansu da wasu mutane sama da 15 da suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Batsari da ke jihar.

‘Yan bindigar da suka mika wuyan sun hada da Abu Radde da Umar Black.

An alakanta mika wuyan nasu da zafafan hare-haren da sojojin hadin gwiwa na Operation fansar yamma da sauran jami’an tsaro ke cigaba da gudanarwa a yankin.

Wasu majiyoyi sun shaidawa gidan talabijin na Channels a ranar Litinin cewa bikin mika wuya da aka gudanar a ranar Lahadi ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da wasu wakilai daga sojoji da shugabannin gargajiya da na addini a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata