Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba da umarnin rufe ayyukan hakar ma’adanai da akeyi ba bisa ka’ida ba a cikin Abuja.
Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Ajao Saka Adewale, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake ganawa da manema labarai sakamakon taron kwamitin tsaro na babban birnin tarayya Abuja da aka gudanar a fadar gwamnatin tarayya da ke ofishin ministan wanda ministan ya jagoranta.
Kwamishinan ya ce, batun hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a kewayen birnin ya kasance abin damuwa, kuma hakan yana da illa ga tsaro da hakan yasa Ministan ya ba da umarnin a rufe duk wasu wuraren hakar ma’adanan nan take.
