Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuShugaba Tinubu ya umurci a rika kula da lafiyar tsoffin ma'aikata masu...

Shugaba Tinubu ya umurci a rika kula da lafiyar tsoffin ma’aikata masu karamin karfi kuma a kara musu fansho

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin gaggauta yin shirin samar da kiwon lafiya kyauta ga ‘yan fansho masu karamin karfi a karkashin shirin CPS, yana mai bayyana shi a matsayin wani muhimmin bangare na kare lafiyar al’umma a yayin ritaya.

Shugaban ya kuma yi kira da a gaggauta karin kudaden fensho da aka dade ba’ayi ba,ba tare da bata lokaci ba tare da yin tsari maikyau da zai taimakawa ‘yan fansho.

Tinubu ya ba da umarnin ne bayan ya samu bayanai daga babbar Daraktar hukumar fansho ta kasa PenCom, Madam Omolola Oloworaran ya kuma umarci shugabar da ta gaggauta warware matsalar fansho da ‘yan sanda suka dade suna yi, yana mai jaddada cewa ‘yan sandan da ke aiki da kuma kare al’umma sun cancanci yin ritaya cikin mutunci da kwanciyar hankali.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata