Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuBa zan yi sulhu da 'yan bindiga ba - Gwamna Umar Bago

Ba zan yi sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamna Umar Bago

Gwamnan jihar Neja, Muhammad Umaru Bago, ya yi alwashin ba zai yi sulhu da ‘yan bindiga ba, yana jaddada cewa hakan ba abu ne da za a amince da shi ba, don haka zai nemi shugaban kasa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro su sa baki kan lamarin yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da ya addabi wasu kananan hukumomin jihar.

A cewar Bago ya lura cewa sulhu da ‘yan bindigar a wasu jihohin Nijeriya ya haifar da karuwar satar shanu a jihohin.

Gwamnan ya bayyana matsayar sa ne a taron masu ruwa da tsaki kan tabbatar da tsaro da duba lafiyar dabbobi da aka gudanar a Minna.

Da yake magana kan yadda mutane ke sayarda naman da suke yankowa daga daji ya bayyana cewa za a samar da matakan da suka dace don tabbatar da ana sayar da nama ne kawai a kasuwannin da ake yankawa da kuma sayar da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata