Daliban Nijeriya uku da suka zama zakaru a gasar TeenEagle Global na shekarar 2025 a fannonin turanci, sun samu kulawar gidauniyar Atiku Abubakar AAF wacce ta ba su tallafin karatu, domin karfafa musu gwiwa.
Daliban da suka hada da Nafisa Abdullahi, Rukaiya Mohammed Fema da Khadija Kashim Kalli, an yi musu haka ne saboda bajintar da suka yi a fannin ilimi a gasar ta kasa da kasa.
Gidauniyar wacce tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya kafa ta ce saboda kwazon su ta ba da tallafin karatun tun daga sauran makarantun sakandare har zuwa jami’a.
A wata wasika data fito daga gidauniyar ta ce tallafin ya kunshi dukkan kudaden da ake kashewa na ilimi har zuwa kammala karatunsu na jami’a, ba tare da la’akari da makarantar da suka zaba ba.

Thanks 👍 so much