Home Labarai An dakatar da sarkin Misau

An dakatar da sarkin Misau

182
0

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya dakatar da sarkin Misau Alh Ahmad Sulaiman da sauran wasu masu rike da sarautun yankin.

Bayan hakan, dama tun farko gwamnatin jihar ta dakatar da jami’an karamar hukumar ta Misau, biyo bayan wani rikicin makiyaya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9 a kauyen Zadawa na karamar hukumar ta Misau.

Gwamna Bala Muhammad ya bayyana dakatarwar a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin da zai binciki musabbabin rikicin.

Yace an dakatar da masu rike da sarautun gargajiya na yankin ne biyo bayan takardar koke da aka gabatar masa a kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here