Wednesday, April 8, 2026
HomeUncategorizedGwamna Zulum ya nada karin masu taimaka masa kan harkokin yada labarai

Gwamna Zulum ya nada karin masu taimaka masa kan harkokin yada labarai

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da nadin Abdurrahman Ahmed Bundi a matsayin babban mai taimaka masa na musamman a fannin jaridu da sadarwa ta zamani (STA).
Kakakin gwamnan, Malam Dauda Iliya ne ya sanar da nadin a Maiduguri babban birnin jihar. 
Abdurrahman Bundi ya kammala karatunsa ne a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2011 sannan ya samu digirinsa na biyu a fannin gudanar da watsa labarai daga Jami’ar Middlesex da ke London.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata