Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuƳan sanda sun kama mutane 288 bisa zargin tada rikici a zaben...

Ƴan sanda sun kama mutane 288 bisa zargin tada rikici a zaben cike gurbi a Kano

Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutane 288 bisa zargin tada rikici da aikata laifuka yayin zaben cike gurbi da aka gudanar a mazabun Ghari/Tsanyawa da Bagwai/Shanono a ranar Asabar, 16 ga Agusta 2025.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an kwato makamai daban-daban daga hannun waɗanda ake zargin, ciki har da:

Kwamishinan ƴan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar za ta ci gaba da bincike don gano masu daukar nauyin waɗanda ake zargin, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

Ya kuma gargadi masu shirin tada fitina ko yin magudi a zaɓen da cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani, yana mai kira ga al’umma da su ci gaba da bin doka da kuma bayar da hadin kai ga jami’an tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata