Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuAPC ta lashe kujeru 12 cikin 16 na zabukan cike gurbin da...

APC ta lashe kujeru 12 cikin 16 na zabukan cike gurbin da aka gudanar a jihohi 12 na Nijeriya

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murna ga ‘yan takarar jam’iyyar APC da suka yi nasara a zabukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, a mazabu 16 da ke jihohi 12 a fadin kasar.

Shugaban kasar ya kuma yaba wa Hukumar zabe INEC bisa yadda zabukan suka gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da rikici ko tashin hankali ba.

A sakamakon da INEC ta bayyana, APC ta lashe mazabu 12, APGA ta samu guda 2, PDP ta samu 1, yayin da NNPP ta lashe guda 1.

Tinubu ya kuma taya sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, murna bisa wannan nasarar farko a karkashin shugabancinsa, tare da jinjinawa gwamnonin APC da sauran shugabannin jam’iyyar kan rawar da suka taka wajen samun nasara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata