Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnatin Tinubu na tunanin karawa masu rike da mukaman siyasa albashi

Gwamnatin Tinubu na tunanin karawa masu rike da mukaman siyasa albashi

Hukumar da ke lura da tattara kudaden shiga da rarrabawa ta kasa RMAFC ta bayyana shirin duba albashin manyan jami’an siyasa a Najeriya, tana mai cewa adadin da ake biya yanzu bai dace da nauyin aiki da yanayin tattalin arziki ba.

Shugaban hukumar, Mohammed Shehu, ne ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu na karɓar Naira miliyan 1.5 a wata, yayin da ministoci ke samun ƙasa da Naira 1m tun daga shekarar 2008.

Sai dai Kungiyar Ƙwadago ta Kasa (NLC) ta nuna adawarta da wannan shiri, tana cewa shirin zai ƙara bambanci tsakanin masu mulki da talakawa, musamman ganin akwai wasu fa’idodi na boye da ’yan siyasa ke ci gaba da amfana da su.

Jaridar Punch ta ruwaito hukumar ta RMAFC na jaddada cewa aikinta ya ta’allaka ne kawai kan albashin ’yan siyasa, ’yan majalisa da na shari’a, ba na ma’aikatan gwamnati ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata