DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya amince da haramta luwadi a rundunar sojin Nijeriya

-

Shugaba Tinubu

An haramta wa jami’an sojin Nijeriya yin luwadi, madigo, sanya kayayyakin da basu dace ba, da sauran abubuwan  da ake ganin sun saba wa ka’idojin rundunar.

Haka zalika an hana jami’an huda jiki da nufin  saka Sarka ko Dan kunne ko kuma zanen hotuna a jikin fata wato  (Tatoo )a jiki, da shan  Barasa a yayin da suke aiki ko basa aiki.

Wannan umurnin yana kunshe ne acikin sashe na 26 na kundun rundunar da aka yi wa kwaskwarima da shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 16 ga Disamba, 2024.

A wata takarda da jaridar Punch ta samu a ranar Asabar wani bangaren ta yana cewa, “Bai kamata jami’in soji su dinga aikata  luwadi, madigo, da sauran munanan ayyuka ba.

 Haka zalika ba a amince wani jami’in rundunar soji ya dunga irin wayannan ayyuka ba ciki harda yin “Tattoo” dama shan abubuwan da zasu kautarwa mutum hankali a loka2cin yana kan aiki ko baya aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Atiku Abubakar ya caccaki hukumar EFCC kan tsare tsohon dan majalisa Gudaji Kazaure

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, kan tsare tsohon dan...

Gwamnatocin Pakistan da Indiya sun amince da tsagaita wuta a Asabar dinnan

Ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ya sanar a shafinsa na X cewa, kasashen sun amince da Shirin tsagaita wuta cikin gaggawa. Shugaba Trump ya sanar...

Mafi Shahara