DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeUncategorized'Yan sanda sun kubutar da mutum 18 da aka sace kan hanyar...

‘Yan sanda sun kubutar da mutum 18 da aka sace kan hanyar Funtua-Gusau

Akalla mutane 18 ne rundunar ‘yan sandan jihar Katsina suka ceto a hannun ‘yan bindiga bayan dakile wani yunkurin garkuwa da mutane a kan hanyar Funtua-Gusau da ke jihar Zamfara.
Rundunar tace ta kuma yi nasarar kwato wasu dabbobi da aka yi yunkurin sacewa a kauyen Gidan Gada dake karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.
Da yake jinjinawa jami’an ‘yan sanda kan wannan kokarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Aliyu Abubakar Musa, ya bukaci al’umma su ci gaba da goyon bayan jami’an tsaro tare da kwarmata musu bayanai.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata