Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuMajalisar dattawan Nijeriya ta ce sai an kammala shari'a kafin Natasha ta...

Majalisar dattawan Nijeriya ta ce sai an kammala shari’a kafin Natasha ta koma bakin aiki

Majalisar dattawan Nijeriya ta ce Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar Kogi ta tsakiya, ba za ta iya komawa kujerarta a zauren majalisar ba duk da cikar wa’adin watanni shida na dakatarwar da aka yi mata.

A wata wasika da mukaddashin magatakardan majalisar Dr. Yahaya Dan Zaria ya rubuta a ranar 4 ga Satumban 2025, majalisar ta tabbatar da cewa ta karɓi sanarwar Natasha kan shirinta na dawowa bakin aiki.

Sai dai majalisar ta ce dakatarwar ta na nan daram har yanzu saboda shari’ar da ake yi a gaban kotun daukaka ƙara, wadda ita kanta Natasha ta shigar domin kalubalantar hukuncin dakatarwar.

An dakatar da Natasha ne a ranar 6 ga Maris, 2025, bayan da aka zarge ta da kin bin umarnin shugabancin majalisar, wanda ya samo asali sakamakon amincewa da sauya kujerarta a lokacin zaman majalisar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata