DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Babu kanshin gaskiya a zancen cewa Kwankwaso zai koma APC – Hashimu Dungurawa na NNPP a Kano

-

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

 Shugaban jam’iyyar NNPP Hashim Sulaiman Dungurawa, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba ga manufofin gwamnatinsa da al’umma ba sa goyon baya, ko kuma ya fuskanci shan kaye a babban zabe mai zuwa.

Dungurawa ya kuma ce batun da ake cewa jagoran jam’iyyar Rabiu Musa Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ba gaskiya ba ne.

Google search engine

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, Dungurawa ya jaddada cewa jam’iyyar NNPP na kara samun tagomashi tare da kara fadada a dukkan jihohin Nijeriya 36, wanda hakan zai basu damar samun kujerun gwamnonin wasu jihohi a zaben 2027.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da hankali wajen aiwatar da manufofin da za su rage wa ‘yan Nijeriya radadin da suke ciki da kuma kauce wa bullo da tsare-tsaren da suka saba wa muradun jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Peter Obi ya bukaci matasa da su nuna kauna da kishin Nijeriya albarkacin ranar masoya

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya, Peter Obi, ya bukaci ’yan Nijeriya musamman matasa su yi bikin ranar masoya ta Valentine cikin nuna kishin ƙasa da...

Nijeriya na da damar jagorantar Afirka ta zama babbar nahiya a duniya – António Guterres

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya bukaci Nijeriya ta jagoranci Afirka wajen neman sauyi a tsarin duniya, yana mai cewa ƙasar na da...

Mafi Shahara