Fadar shugaban kasa ta ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na tafiya kan madaidaiciyar hanya, tana mai musanta ikirarin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da ya ce yunwa ta addabi ‘yan Najeriya.
Mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, inda ya ce gwamnatin na samun ci gaba sannu a sannu.
A ranar Litinin, Atiku ya soki gwamnatin Tinubu, inda ya ce sama da shekaru biyu da hawa mulki bai nuna iya shawo kan yunwa da talauci da ke addabar kasa ba. Ya bayyana cewa matalauta da talakawa ne suka fi shan wahala daga wannan hali.
Sai dai a martanin sa Onanuga ya ce ikirarin Atiku cewa yunwa ta addabi Najeriya tare da kwatanta halin da ake ciki da tarzomar Faransa ta 1789 da juyin juya halin Bolshevik na Rasha a 1917 ba daidai ba ne.
