Wani mutum ya rasa ransa a lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari a wani wurin hakar ma’adinai a ƙauyen Kokamba, cikin yankin Magami na ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Shaidu gani da ido sun ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe 1:30 na rana, inda maharan suka bude wuta kan masu hakar ma’adinai ba kakkautawa, kafin su tsere zuwa dajin da ke kusa da su.
Jaridar The Guadian ta rawaito cewa rahotanni sun nuna cewa an hango fitaccen dan bindiga Bello Turji a dajin Kalage, da ke yankin Mashema a gabashin Kagara, jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin mai suna Abubakar Ibrahim ya bayyana cewa an kai gawar mamacin wani ƙauye da ke kusa, lamarin da ya jefa jama’a cikin tsoro da fargabar yiwuwar mayar da martani kan al’ummar Fulani.
Hukumomin tsaro dai sun roƙi jama’a da su kwantar da hankulansu tare da ba da haɗin kai, ta hanyar sanar da duk wani motsi da ake zargi domin samun damar kamo maharan.
