Kwararru a fannin noma sun bayyana cewa mutum biyu a cikin 11 na fama da yunwa kullum a Najeriya.
Masanan sun kuma ce mutum daya a cikin ‘yan Afirka biyar na fuskantar yunwa a kullum, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Babban jami’in shirin bunkasa noma a nahiyar Afirka, mai kula da Najeriya Onijighogia Emmanuel shi ne ya bayyana haka yayin wani taron bayar da horo.
A cewar sa, akwai bukatar sa hannu daga gwamnatoci, manoma da kuma kungiyoyin fararen hula wajen inganta bangaren noma a nahiyar Afirka baki daya.
