Kungiyar malaman jami’o’i na Nijeriya ASUU ta yanke shawarar fara yajin aiki na tsawon makonni biyu daga ƙarfe 12 na dare na ranar Litinin, 13 ga Oktoba, 2025, idan har gwamnati ba ta nuna gaggawar magance ƙorafinta ba.
A taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar ASUU a Jami’ar Abuja, shugaban kungiyar, Prof. Chris Piwuna, ya zargi gwamnati da rashin gaskiya a tattaunawar da aka yi a baya, inda ya ce an bar ƙorafe-ƙorafensu ba a bi su ba.
An ba gwamnati wa’adin kwanaki 14 tun daga makon da ya gabata don ta warware matsalolin da kungiyar ta lissafa, ciki har da aiwatar da yarjejeniyar 2009 da sauran batutuwa.
A cikin memo ɗin “Strike Bulletin One” da aka raba ga rassan kungiyar, an umurci dukan malaman jami’o’i su dakatar da ayyukansu a lokacin yajin aiki.
ASUU ta ja hankalin jama’a cewa wannan ba yunkuri ne na jin haushi ba, amma domin tilasta gwamnati ta dauki matakan da suka dace don inganta tsarin jami’o’in gwamnati da kula da walwalar malamai.
