Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnatin Nijeriya ta yi barazanar hana ASUU albashi idan ta tafi yajin...

Gwamnatin Nijeriya ta yi barazanar hana ASUU albashi idan ta tafi yajin aiki

Gwamnatin Nijeriya ta ja kunnen ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, wato ASUU, cewa za ta aiwatar da tsarin “ba aiki, ba albashi” idan malaman suka tafi yajin aikin da suka ayyana.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ba za ta ci gaba da biyan ma’aikatan da suka dakatar da aiki ba, tare da jaddada cewa gwamnati ba za ta amince da amfani da yajin aiki wajen tilasta mata amincewa da bukatu ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sai dai ASUU ta mayar da martani, tana cewa wannan barazanar ba ta dace ba, domin gwamnati ce ke jinkirta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma tun da dadewa, ciki har da batun albashin da bai daidaita ba da kuma gyaran jami’o’in ƙasa.

Ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta sanar, wanda zai fara daga ranar Litinin 13 ga Oktoba, muddin gwamnati ba ta ɗauki matakin da ya dace ba.

Masu lura da al’amura sun yi gargadin cewa wannan sabuwar takaddama tsakanin gwamnati da ASUU na iya sake jefa ɗalibai cikin tsaikon karatu, yayin da malaman kuma za su iya rasa albashinsu idan aka aiwatar da manufar “ba aiki, ba albashi”.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata