An cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin shugabannin al’umma da wasu ’yan bindiga a kananan hukumomin Malumfashi, Funtua da Bakori ta Jihar Katsina domin dakile hare-hare da sace-sacen mutane da ke ci gaba da addabar yankin.
Taron sulhun wanda aka gudanar a ƙauyen Kakumi na ƙaramar hukumar Bakori ya haɗa wakilan al’umma da wasu shugabannin ’yan bindiga, inda aka tattauna hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin jama’a da ’yan bindigar.
Majiyoyi sun ce wasu daga cikin shugabannin ’yan bindigar sun yi alkawarin daina kai hare-hare da sauran ayyukan ta’addanci a yankunan da abin ya shafa daga ranar Lahadi, 12 ga Oktoba kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wannan mataki na cikin shirin gwamnatin jihar na dawo da zaman lafiya da farfaɗo da harkokin noma, kasuwanci da sauran ayyukan tattalin arzikin karkara da rikice-rikice suka durƙushe. Haka kuma, sarakuna, dattawa da jami’an tsaro sun halarci taron suna mai kira da a mutunta yarjejeniyar don dorewar zaman lafiya.
