Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuBa da jimawa ba tsananin da ‘yan Nijeriya ke ciki zai zama...

Ba da jimawa ba tsananin da ‘yan Nijeriya ke ciki zai zama sauki – Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce matsin tattalin arzikin da ake ciki yanzu zai zo karshe nan ba da jimawa ba, domin ƙasar na kan hanyar shiga sabon mataki na wadata da bunƙasar tattalin arziki.

Shettima ya bayyana haka ne a taron Nigeria Renewable Energy Innovation Forum NREIF da aka gudanar an Abuja a ranar Talata.

Haka kuma ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tare da ‘yan ƙasa kuma yana jin raɗaɗin halin da suke ciki, yana mai cewa gwamnati ta ɗauki matakan da za su tabbatar da ci-gaba mai ɗorewa.

A cewarsa, Zuciyar Shugaban Ƙasa na tare da ‘yan Nijeriya duk da ƙalubalen da ake fuskanta, sannan ya tabbatar da cewa an wuce mawuyacin hali, kuma ana kan hanyar samun sauki da ci-gaba.

Rahoton Daily Trust ya ce taron wanda hukumar samar da wutar lantarki ta karkara REA ta shirya shi ne domin neman masu saka hannun jari a cikin masana’antar samar da makamashi mai sabuntawa a cikin gida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata