DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Amurka na shirin kakaba takunkumi ga gwamnonin Arewa 12 da wasu sarakunan gargajiya

-

Gwamnonin Arewa 12 da wasu sarakunan gargajiya da ma wasu manyan alkalai sun shiga cikin wata sabuwar ce-ce-ku-ce ta diflomasiyya bayan Majalisar dokokin Amurka ta fara nazarin wani kudiri da zai iya sanya musu takunkumi.

Amurka ta na zarginsu da hannu a kisan kiyashi kan Kiristoci da cin zarafi ta hanyar dokokin shari’a da batun raina addini a Nijeriya.

Google search engine

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai damuwa ta musamman tare da umartar sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da ya dauki mataki cikin lokaci.

Kudirin da Sanata Ted Cruz ya dauki nauyi, mai suna “Nigeria Religious Freedom Accountability Act 2025”, yana neman sanya takunkumi kan manyan jami’an gwamnati, sarakuna, da alkalai da ake zargi da amincewa ko tallafawa cin zarafi kan Kiristoci da sauran ƙananan ƙungiyoyin addini kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

Idan aka amince da kudirin, za a iya sanya musu takunkumin hana visa, toshe asusun banki da sauran takunkumin kudi bisa tsarin dokar Global Magnitsky, musamman ga gwamnonin jihohi 12 da suka aiwatar da dokar Shari’a mai cike da sabani a tsakanin Kiristoci da Musulmi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwankwaso ya bayyana masu digirin digirgir “Phd” 300 da Gidauniyar Kwankwasiyya ta samar a taronta na shekara-shekara

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana sama da masu digiri na uku (PhD) 300 da aka samar ta hanyar...

Gwamnatin Kano ta haramta biyan haraji da tsabar kudi daga 1 ga watan Janairu

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa daga 1 ga Janairu, 2026, ba za a amince da biyan haraji da tsabar kuɗi ko takardar banki...

Mafi Shahara