Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedCole Palmer ya karya tarihin Yaya Toure na cin bugun daga kai...

Cole Palmer ya karya tarihin Yaya Toure na cin bugun daga kai sai mai tsaron raga a Firimiya

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Cole Palmer ya kafa sabon tarihi a gasar Firimiyar Ingila, inda ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a bugun fanareti a tarihin gasar. 

Dan wasa Palmer ya kafa sabon tarihin ne, a wasan da Chelsea ta samu nasara da ci 4 da 3 a kan Tottenham, inda ya zura kwallaye biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida da suka zama cikamakin kwallaye 12 na bugun fanareti a jere. 

Wannan bajinta ta zarce ta fitaccen dan wasa Yaya Toure, wanda a shekarar 2010 ya zura wa kungiyar Manchester City kwallaye 11 a jere a bugun daga kai sai mai tsaron gida ba tare da ya zubar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata