Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana takaicin ta kan sace wasu daliban makarantar St. Mary’s da ke yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara, lamarin da ya faru duk da gargadin tsaro da aka riga aka bayar a yankin. Har yanzu hukumomin tsaro ba su tabbatar da adadin waɗanda aka sace ba, yayin da bincike da kokarin ceto su ke ci gaba.
A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Neja Abubakar Usman ya sanya wa hannu, gwamnatin jihar ta ce tun kafin faruwar lamarin ta samu rahotannin ƙarin barazanar tsaro a wasu sassan Neja ta Arewa, wanda ya sa ta dakatar da ayyukan gine-gine tare da rufe dukkan makarantun kwana na yankin. Sai dai duk da wannan umarni, makarantar St. Mary’s ta buɗe ba tare da sanarwa ko neman izinin gwamnati ba, abin da ya jefa dalibai da malamai cikin haɗari.
