Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedA gaggauta kamo wadanda suka kashe basaraken Chanchanji - Gwamnan Taraba

A gaggauta kamo wadanda suka kashe basaraken Chanchanji – Gwamnan Taraba

Gwamnan jihar Taraba Agbu Mefas ya bada umurnin a gaggauta kamo waɗanda suka kashe basaraken garin Chanchanji da ɗan sa.

A sanarwar da kakakin gwamnan Emmanuel Bello ya fitar ta nuna cewa gwamnan ya jajanta wa iyalan basaraken da ilahirin jama’ar ƙaramar hukumar Takum kan wannan aika aika.

Sarkin mai suna Kumbiya Tanimu da ɗan sa Yusuf sun gamu da ajalinsu ne a hanyar Chanchanji zuwa Takum bayan sun halarci wani jana’iza a hanyar komawa gida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata