Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, ya caccaki kawancen Atiku, inda ya ce babu wanda ke magana a kansu sai ‘yan Abuja
Dalori ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Talata, inda ya ce APC ta riga ta samu karbuwa tun bayan hadewar jam’iyyu da suka kafa ta, kuma ba wani abu sabo da kawancen zai iya kawowa.
Game da rade-radin cewa APC na cikin rikici bayan taron shiyyar Arewa maso Gabas da aka yi a Gombe da ya rikide zuwa hatsaniya, jaridar Daily Trust ta ambato shi yana jaddada cewa babu wata matsala da za ta raba kan mambobin jam’iyyar a kasa.
