Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuADC ta bukaci Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Katsina da Zamfara

ADC ta bukaci Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Katsina da Zamfara

Jam’iyyar ADC ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihohin Katsina da Zamfara, bayan hare-haren Malumfashi da suka yi sanadiyyar mutuwar gwamman mutane cikin watanni biyu.

Jam’iyyar ta ce kashe-kashen da suka hada da harbin mutane 30 a masallaci da kuma kona gidaje da mutanen ciki a Katsina, tare da sace-sacen jama’a a Zamfara, sun tabbatar da gagarumar gazawar tsarin tsaro.

Rahotonni da jaridar Punch ta tattaro hadakar jam’iyyar ta ADC Ta soki Shugaba Tinubu da zargin fifita yawon kasashen waje da daukar hoto maimakon kare ‘yan kasa, tare da jaddada cewa gwamnatin tarayya na bukatar sake duba tsarin tsaro da gaggawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata