Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuADC ta zargi INEC da shirin hana ta tsayar da ‘yan takara...

ADC ta zargi INEC da shirin hana ta tsayar da ‘yan takara a 2027

Jam’iyyar ADC ta zargi Hukumar Zaben Nijeriya (INEC) da ƙoƙarin hana ta tsayar da ‘yan takara a zaɓen 2027.

A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce matakan da INEC ke ɗauka na iya hana ta cika ƙa’idojin doka na zaɓe.

Rigimar ta samo asali ne daga matakin INEC na ƙin karɓar wasu takardu daga jam’iyyar, tana mai cewa tana jiran hukuncin kotu kan rikicin shugabancin ADC.

Sai dai jam’iyyar ta ce wannan mataki na barazanar hana ta cika sharuddan doka, musamman wa’adin kwanaki 21 da dokar zaɓe ta tanada kafin gudanar da wasu muhimman ayyuka.

ADC ta bayyana cewa INEC ta riga ta sanya ranar 10 ga Mayu a matsayin wa’adin ƙarshe na miƙa takardu, amma ƙin karɓar bayanan jam’iyyar zai sa ta kasa bin wannan ƙa’ida.

Jam’iyyar ta kuma ce a baya INEC ta amince da shugabancin da ke akwai, inda ta sanya ido kan taron kwamitin zartarwa na ƙasa tare da sabunta bayananta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata