Gwamnatin Nijeriya ta yi karin haske kan rahoton da kamfanin KPMG ya fitar game da sabbin dokokin haraji, inda ta ce yawancin batutuwan da kamfanin ya kalla a matsayin kura-kurai ko gibi ba daidai ba ne, sai dai rashin fahimta da kuma bambancin ra’ayi kan manufar gyaran tsarin haraji.
A cikin sanarwar da kwamitin sabunta dokokin haraji na fadar shugaban kasa ya fitar, gwamnati ta ce sabbin dokokin haraji sun bi ka’idojin duniya ne don tabbatar da gaskiya, daidaito da hana zamba.
Gwamnatin ta jaddada cewa matakan da ta dauka kamar harajin riba daga hannun jari, takaita amfani da kasuwar bayan fage wajen sayen daloli, da kuma sharadin VAT ga duk harkar da ba a bi doka ba, duk wani yunkuri ne na tsabtace tsarin haraji da karfafa tattalin arziki.
DCL Hausa ta rawaito cewa gwamnati ta ce KPMG ta yi watsi da muhimman sauye-sauyen da sabbin dokokin suka kawo, ciki har da rage harajin kamfanoni daga kashi 30% zuwa 25%, karin fa’idodin VAT ga ‘yan kasuwa, tallafin kananan masana’antu da masu karamin karfi, da kuma kawar da harajin minimum tax.
Gwamnatin ta ce gyaran dokokin haraji babban mataki ne da zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikin Nijeriya.
Gwamnati ta bukaci kamfanoni da masana su koma ga tattaunawa mai ma’ana domin tabbatar da ingantaccen aiwatar da sabbin dokokin haraji.
