Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuAkwai wariya ga Arewacin Najeriya a gwamnatin Tinubu — Bashir Dalhatu

Akwai wariya ga Arewacin Najeriya a gwamnatin Tinubu — Bashir Dalhatu

Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana damuwarta kan yadda yankin Arewa ke fuskantar wariya wajen rabon kasafin kuɗi da aiwatar da manyan ayyuka a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban kwamitin amintattu na ACF, Alhaji Bashir M. Dalhatu, ne ya bayyana haka a taron tattaunawa da Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation ta shirya a Kaduna.

Dalhatu ya ce abin takaici ne ganin yadda ake yi wa yankin Arewa watsi da muhimman ayyukan ci gaba duk da irin gudunmuwar da yankin ya bayar wajen nasarar Tinubu a zaben 2023.

Ya jaddada cewa wannan lamari rashin adalci ne ga yankin da ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa wannan gwamnati.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata