Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuAmbaliya ta yi ajalin mutane 165, tare da ɗai-ɗaita 119,000 a bana...

Ambaliya ta yi ajalin mutane 165, tare da ɗai-ɗaita 119,000 a bana – Hukumar agaji ta NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta bayyana cewa mutane 165 ne suka rasa rayukansu, yayin da 82 suka bace, kuma sama da mutane 119,791 ne ambaliya ta shafa a bana.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin rahoton bayanan kididdiga da hukumar ta fitar ranar Juma’a.

NEMA ta ce har ila yau, mutane 138 sun jikkata, 43,936 sun rasa matsuguninsu, gidaje 8,594 sun lalace, sannan filayen noma 8,278 sun lalace a ƙananan hukumomi 43 a jihohi 19 na ƙasar.

Rahoton ya kuma nuna cewa mafi yawan waɗanda lamarin ya fi shafa mata ne da ƙananan yara.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata