Thursday, April 9, 2026
HomeKetareAn cafke diyar tsohon shugaban kasar Tunisiya Ben Ali a Faransa

An cafke diyar tsohon shugaban kasar Tunisiya Ben Ali a Faransa

Halima Ben Ali, ’yar tsohon Shugaban Tunisiya Zine El Abidine Ben Ali wanda aka kifar da gwamnatinsa a shekarar 2011 lokacin Arab Spring, an cafke ta a ƙasar Faransa bisa bukatar hukumomin Tunisiya ga kasar.

Rahoton jaridar TRT Afrika ya ce jami’an shari’a na Faransa sun shaida wa AFP cewa an kama Halima a filin jirgin Charles de Gaulle da ke birnin Paris yayin da take shirin hawa jirgi zuwa Dubai.

Rahoton ya ce za ta bayyana gaban ofishin mai gabatar da ƙara na Paris a ranar Laraba domin sanar da ita bukatar da aka samu na kama ta na wucin gadi daga hukumomin Tunisiya.

Bayan haka, za a iya tura ta zaman jiran shari’a a kurkuku kafin mika wa hukuma ko kuma a ci gaba da bin diddigi a ƙarƙashin kulawar shari’a, in ji sanarwar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata