Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Saudiyya ta sanar da dokar hana daukar hoto ko bidiyo ko kuma alamomi na siyasa a manyan wuraren aikin Hajji.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce an haramta daukar hotuna ko daukar bidiyo a cikin Masallacin Harami na Makkah, da Masjid an-Nabawi a Madina, da kuma muhimman wuraren aikin Hajji da suka hada da Mina, Arafat, da Muzdalifah.
Jami’ai sun jaddada cewa irin wadannan ayyuka na iya gurgunta yanayin aikin Hajji da kuma rarrabuwar kawuna a tsakanin mahajjatan da suka fito daga sassan duniya.
